'Yan sandan Afghanistan sun karbi iko da Bamiyan

Kasar Afghanistan ta soma yunkurin karbar iko da tsaron kanta, inda lardin Bamiyan ya zamanto na farko da dakarun kungiyar tsaro ta NATO suka mika wa yansandan Afghanistan.

Ministocin Gwamnatin Afghanistan da kuma jakadun kasashen waje sun tashi ta jirgin sama zuwa lardin tsakiyar kasar daga Kabul babban birnin kasar domin bukin mika lardin.

Wakilin BBC a Afghanistan ya ce Bamiyan na daya daga cikin lardunan da suka fi zaman lafiya , to amma mazaunansa da yawa na tsoron cewar mika ikon zai iya haddasa karin cin hanci da kuma rashin tsaro.