Kasar China na fushi da Amurka

Obama ya gana da Dalai Lama Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dalai Lama da Shugaba Obama

Kasar China ta mayar da martani cikin fushi akan ganawar da aka yi tsakanin shugaban Amurka Barack Obama da shugaban yankin Tibet Dalai Lama.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta China ta bayyana ganawar da suka yi a Washington a matsayin wani shisshiga akan harkokin cikin gidanta.

Sai dai fadar gwamnatin Amurka ta ce ganawar ta jaddada muhimmancin da Shugaba Obama ke bayarwa wajen ganin an adana tarihi, da al'adu da kuma harshen kabilar Tibet tare da kare hakkin bil'adama.

China na yiwa Dalai Lama kallon wani mai raba kawunan jama'a, wanda ke son ganin an kawo karshen mulkin da China ke yiwa yankin Tibet.

Sai dai ya sha musanta hakan, inda ya ke cewa yana so ne kawai yankin ya samu 'yancin kansa.