Gwamnan Borno ya amince cewar soji na yin azarbabi a aikinsu

Hare haren Boko Haram Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hare haren Boko Haram

Gwmnan Jihar Borno da ke fama da boren kungiyar masu kishin Islaman nan ta Boko Haram, ya amince cewa sojoji na wuce makadi da rawa a yakin da suke yi da 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Gwamna Kashim Shettima ya shedawa BBC cewar za'a biya diyya ga duk wadanda suka rasa gidajensu da abubuwan hawa a tashin hankalin.

Gwamnan ya ce za a samar da layukan tarhon da mutane za su rinka gabatar da kokensu, sannan ya roki mutanen da ke barin garin da su koma.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na zargin rundunar sojin kasar da kisan gilla a artabun da suke yi da 'yan Boko Haram