'Mubarak bai shiga halin rai kwakwai mutu kwakwai ba'

Gidan Talabijin na Masar ya bada labarin cewa hambararren shugaban kasar Hosni Mubarak ya fita daga hayyacinsa.

Gidan Talabijin din ya ruwaito lauyan Mubarak ya na cewa lafiyarsa ta tabarbare sosai a asibiti inda ake tsare da shi. Wakilin BBC ya ce, sai dai kuma tuni shugaban asibitin ya musanta abun da lauyan Mubarak din ya ce, yana mai cewa lafiyar tsohon shugaban kasar ba ta tabarbare ba.

Kuma wani likita a asibitin ya ce, ai dama tsohon shugaban ya kan fita daga hayyacinsa daga lokaci zuwa lokaci saboda haka babu abunda ya sauya.

A farkon watan Ogusta ne aka shirya za'a yi wa tsohon shugaban shara'a a bisa zargin kashe masu zanga zanga da kuma cin hanci da rashawa.