An cafke Rebbekah Brooks wata ta hannun daman Rupert Murdoch

Rebecca Brooks Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rebecca Brooks

'Yan Sanda a Birtaniya sun tsare Rebekkah Brooks wadda ta ajjiye aikinta a matsayin shugabar kamfanin News Inaternational na hamshakin attajirin nan Rupert Murdoch.

Tsare ta nada nasaba ne da binciken zargin satar sakonni ta waya da cin hanci da rashawa da ake yiwa 'yan jaridar kamfanin.

Ita ce jami'a mafi girman mukami da aka cafke kawo yanzu a abun kunyan nan da ya ci Jaridar News of the World.

Wakilin BBC ya ce, Rebekkah Brooks na da kusanci sosai da manya a Burtaniya, cikinsu har da Firayim Minista David Cameroon .