Asarar rayuka a hadarin mota a Abuja

Abuja a taswirar Najeriya
Image caption Abuja a taswirar Najeriya

A Najeriya, mutane akalla 20 ne suka rasa rayukansu, a wasu hadurran mota guda biyu a unguwar Kugbo, wadda ke kusa da babban birnin Tarayya Abuja, a kan hayar zuwa Keffi.

Hukumar ba da agajin gaggawa a kasar, wato NEMA, ta ce wasu mutanen goma kuma sun jikkata, bayan da wata babbar mota dauke da kayan karfe ta bi ta kan wasu kananan motoci guda takwas.

Kididdiga dai ta nuna cewa hadarin mota na cikin dalilan da ke haddasa yawan mace-mace a tsakanin al'ummar Najeriya.

Abubuwan da ke janyo yawan hadurran motar a Najeriyar sun hada da rashin kyaun hanyoyi, da gangancin tuki, da dai sauransu.