David Cameron na ziyara a nahiyar Afirka

Cameron ya isa kasar Afirka Ta Kudu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption David Cameron

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron ya isa Afirka Ta Kudu a ziyarar kwanaki biyu da ya fara a nahiyar Afirka.

Firayim Ministan na ziyarar ce shi da wadansu manyan 'yan kasuwar Burtaniya, kuma batun kasuwanci tsakanin nahiyar da sauran kasashen duniya ne zai kankane ziyarar ta sa.

A wani sharhi da ya rubuta a jaridar Business Day da ake bugawa a Afirka Ta Kudu Mista Cameron ya ce kasuwanci ne kawai zai magance talaucin da jama'ar nahiyar ke fama da shi.

Ya kara da cewa bai kamata kasashen su rika dogara da tallafin da suke samu daga wajen sauran kasashen duniya ba.

Mista Cameron zai kammala ziyarar ta sa ce a Najeriya.