Janar Petraeus ya sauka daga mukaminsa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption David Petraeus

Kwamandan sojojin Amurka a rundunar tsaro ta NATO da ke Afghanistan Janar David Petraeus, ya sauka daga mukaminsa inda ya mika ragamar jagorancin rundunar ga John Allen.

Janar Petraeus ya bar mukamin ne a lokacin da ake fuskantar kalubalen tsaro sosai a Afghanistan domin ko da a karshen makon jiya sai da aka kashe dan uwan shugaban kasar, yayin da a ranar Lahadi aka kashe wani jami'i da ke aiki a fadar shugaban kasar.

A bara ne dai aka nada Janar Petraeus akan mukamin bayan saukar Janar Stanley McCrystal.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu sauki wajen yawan hare-haren da 'yan kungiyar Taliban ke kaiwa a kasar cikin shekarar da ta gabata, amma duk da hakan yawan mutanen da suka mutu a bana yafi na wadanda suka mutu a bara.

A watan Satumba Janar Petraeus zai fara aiki a matsayin sabon shugaban Hukumar Leken Asirin Amurka, wato CIA.