Bikin tunawa da ranar haihuwar Mandela

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Nelson Mandela tare da iyalansa

Al'ummar kasar Afrika ta kudu na bikin murnar tunawa da ranar haihuwar tsohon shugaban kasarsu, Nelson Mandela wanda ya cika shekaru 98 da haihuwa.

Gidauniyyar taimakon daya kafa ta bukaci al'ummar kasar da suyi aikin agaji na tsawon mintuna 67 , domin tunanawa da gwagwarmayar siyasa da ya yi na tsawon shekaru 67.

Mandela dai zai yi murnar ranar ne tare da iyalansa a kauyensu dake Qunu a gabashin Cape.

Milliyoyin yaran makaranta ne suka yi mishi wakar tunawa da rainar haihuwa a lokaci guda.

Wakar tunawa da ranar Madiba, an rera ta ne a duk makarantun da ke kasar.

Mista Mandela, ya zama jarumi ga dubbin 'yan kasar Afrika ta kudu, saboda fafutukar da yayi da turawan mulkin mallaka a kasar.

Tarihi

An tsare shi tsawon shekaru 27, amma daga bisani ya zamo shugaban kasar bakar fata na farko inda ya taka rawa wajen samar da zaman lafiya. Ya samu kyautar zaman lafiya ta Novel a 1993.

Tun bayan da ya sauka daga shugabancin kasar a 1999, Mr Mandela ya zamo mafi shahara a Afrika ta Kudu, yana yaki da cutar kanjamau, sannan ya samar wa kasar damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya ta 2010.

Mandela ya taka rawa wajen samar da zaman lafiya a kasashen Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Burundi da wasu kasashen Afrika.

Mandela ya kaurace wa rayuwa a bainar jama'a a shekara ta 2004, yana mai shekaru 85 domin bai wa iyalinsa isasshen lokaci.

"Kada ku kirani, zan kira ku," kamar yadda ya gargadi duk wanda ke son gayyatarsa wani taro.

An haifi Mandela a shekarar 1918, kuma dan kabilar Madiba ne a wani karamin kauye da ke Cape. Ana yi masa lakabi sa sunan kabilarsa ta Madiba.

Mahaifinsa ya rasu lokacin yana da dan shekara tara.

Siyasa

Ya shiga jam'iyyar African National Congress ANC, a 1943, inda ya zamo shugaban matasa, kafin daga bisani ya zamo shugabanta.

Mandela ya yi karatun lauya sannan ya bude kamfanin aikin lauya tare dea abokinsa Oliver Tambo.

Kuma a tare ne suka yi fafutukar yaki da wariyar launin fata wanda jam'iyyar National Party ta fararen fata ta jagoranta.

An tuhumi Mandela da laifin cin amanar kasa a lokuta daban-daban tare da wasu mutanen da dama.

A shekarar 1960, aka haramta jam'iyyar ANC, daga nan kuma Mandela ya koma gefe guda. Daurin rai-da-rai

Mandela wanda shi ne mataimakin shugaban kasa, ya kaddamar da kamfedin zagon kasa ga tattalin arzikin kasar.

Hukuncin dauri

An kama shi sannan aka tuhume shi da laifin yi wa kasa zagon kasa da kuma neman kifar da gwamnati.

Mandela ya nace cewa burinsa shi ne na samar da tsarin dimokradiyya inda jama'a za su zauna da juna cikin kwanciyar hankali da kuma daidaito.

"Wannan shi ne abin da muke son tabbatarwa. Amma idan ta kama zan iya mutuwa kan wannan bukatar".

Kuma an yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai a shekarar 1964.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An daure Nelson Mandela a gidan fursuna na tsawon shekaru 27.

A daidai lokacin da Mandela da sauran 'yan fafutuka su ke tsare, matasa sun ci gaba da fafutukar da suka fara. An kuma kashe daruruwan 'yan makaranta da dama.

Matsin lambar da aka sa ya sa a 1990, shugaba FW de Klerk ya janye haramcin da ya sanya wa ANC, sannan aka saki Mandela daga kurkuku. Kyautar Nobel ta zaman lafiya

A 1992, Mr Mandela ya saki matarsa, Winnie, bayan da aka same ta da laifin sace jama'a da cin zarafi.

Kyautar Nobel

A watan Disamban 1993, aka bai wa Mr Mandela da Mr de Klerk kyautar Nobel ta zaman lafiya.

Watanni biyar bayan haka, a karon farko a tarihin kasar, dukkan kabilu da jinsina suka yi zabe inda Mr Mandela ya zama shugaban kasa.

Mandela ya taka rawar gani wajen farfado da kimar kasar a idon shugabannin kasashen duniya.

Ya kuma taimaka sosai wajen yakar cutar HIV a kasar, inda ya bayyana cewa cutar ce ta kashe dansa.

Ya kuma taka rawa wajen ganin kasar ta samu damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2010.