Murdoch na fuskantar kalubale daga wasu kasashe

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rupert Murdoch

Attajirin nan mai gidajen yadda labarai, wato Rupert Murdoch na fuskantar matsin lamba, saboda badakalar satar bayanai ta wayoyin salula da wasu 'yan jarida dake aiki a wasu daga cikin kamfanoninsa suka yi a a Burtaniya.

A yanzu haka dai Attajirin na fuskantar kalubale wajen hulda da wasu kasashe.

BBC ta samu bayanan da ke nuni da cewa, hukumar tsaro ta FBI a Amurka ta gana da jami'an tsaro a Burtaniya, domin tattaunawa akan binciken da ake yiwa wasu daga cikin 'yan jaridar dake yiwa jaridar News of the World aiki.

Ana dai zargin wasu daga cikinsu da biyan 'yan sanda kudi domin samun bayanai akan mutane.

Hedikwatar kamfanin Mista Murdoch na News Corporationa na kasar Amurka ne, inda kasar ke tsauraran dokokin kan ba jami'ai cin hanci.

A kasar Austrailia ma, hanayen jarin da attajirin ya mallaka na ta zuwa kusa a kasuwar hanayen jari, saboda badakalar satar bayanan.