Allen ya karbi Petraeus a Afghanistan

Janar John Allen na sojin Amurka, ya karbi jagorancin sojin kasashen kawance a Afghanistan daga hannun Janar David Petraeus, wanda shi kuma zai zama jagoran Hukumar Leken Asiri ta Amurka, CIA.

A wajen bukin mika ikon rundunar,Janar Allen ya ce,ya hango tsayraran ranaku a gaba, kuma ba ya da wani tunanin samun sauki a kalubalen da ke a Afghanistan.

Sauyin jagorancin ya zo ne yayinda dakarun kungiyar tsaro ta NATO ta soma mika ikon wasu yankuna ga takwarorinsu na Afghanistan.

To amma har yanzu akwai sauran damuwa game da sha'anin tsaro; da safiyar yau wani bam da aka dana a gefen titi ya halaka wasu sojojin kungiyar tsaron ta NATO 3 a gabacin kasar.

Sannan a cikin makon da ya gabata an kashe wani na hannun daman Shugaba Hamid Karzai, haka nan kuma an kashe kanen Shugaban.

Sai dai kisan da aka yi wa kanen shugaba Karzai da kuma wani mai ba shi shawara, ya nuna girman kalubalen tsaron da ake ci gaba da fama da shi.

A bara ne dai aka nada Janar Petraeus akan mukamin bayan saukar Janar Stanley McCrystal.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu sauki wajen yawan hare-haren da 'yan kungiyar Taliban ke kaiwa a kasar cikin shekarar da ta gabata, amma duk da hakan yawan mutanen da suka mutu a bana yafi na wadanda suka mutu a bara.

A watan Satumba Janar Petraeus zai fara aiki a matsayin sabon shugaban Hukumar Leken Asirin Amurka, wato CIA.