Wasu mahara sun sarewa wata mata hannu a Gusau

Image caption Fatima Muhammed har yanzu na jinya a asibiti

Y'an Sanda a jihar Zamfarar Najeriya sun ce har yanzu ba su kama kowa ba daga cikin wasu matasa maza uku da ake zargi da sare hannun watan mata yar shekaru 21 kwannaki kafin bikin aurenta.

Fatima Muhammad dai ta rasa hannunta na hagu ne a cikin wani hari da aka kai mata da adda a Unguwar kofar Jange babban birnin jahar Gusau.

Wata majiya dai tace maharan na zargin matar ne da zama mai kyakyasawa yan sanda bayanai amma rundunar 'yan sanda tace bata da masaniya da hakan.

A cewar matar wadda ta rasa hannunta na hagu maharran sun tare ta ne sa'adda take kan hanyar ta zuwa kasuwa kuma sun nufi sare kan ta ne da adda amma sai ta kara hannunta abin ya sanya hannun nata ya fadi nan take.

Lamarin dai ya faru ne ana sauran kwanaki goma sha biyu a daura mata aure.

Rundunar yan sanda jahar ta Zamfara dai tabakin kakakinta ASP Sanusi Amiru tace tana cikkakar masaniyar kan faruwar lamarin.

Sai dai har yanzu bata kama kowa ba daga cikin wadanda ake zargi da sare hannun matar.

Koda yake kama wadannan suka yi wannan aika-aikar da kuma hukun tasu idan aka same su da laifi zai sanyaya zuciyar Fatima da danginta amma ga alama hakan ba zai iya kankare tabon da rasa hannun nata zai bar mata a zuci ba.