Shugaban kasar Guinea ya nemi a zauna lafiya

Image caption Shugaban kasar Guinea, Alpha Conde

Shugaban Guinea, Alpha Conde, ya nemi cewa a zauna lafiya a kasar, kuma a hada kai, bayan wani hari da aka kai a gidansa dake babban birnin kasar Conakry.

An dai yiwa gidan ruwan harsasai ne da sanyi safiyar yau dinan. Mutum guda ne ya rasa ransa sanadiyar harin.

Har yanzu dai ba'a san ko su wanene suka kai harin ba.

An dai rufe hanyar zuwan gidan shugaban kasar a yayinda jami'an tsaro suke ci gaba da bincike.

Mazauna birnin na Conakry suke kulle kansu a gidajensu saboda fargabar barkewar rikici.

Mista Conde ya zama shugaban kasa ne bayan zaben watan Disamba da aka gudanar a kasar.

Sojoji ne dai suka yi mulkin kasar na tsawon shekaru biyu kafin Conde ya zama shugaban kasa.