Isra'ila ta karkatar da jirgin ruwan da ya nufi Gaza

Image caption A kwanaki baya ma Isra'ila ta tsare wani jirgin ruwa daya taso daga Turkiya, abun da kuma ya yi sanadiyar mutuwar wasu.

Sojojin Isra'ila sun tsare wani jirgin ruwan Faransa dake kan hanyarsa zuwa zirin Gaza domin kai agaji.

Isra'ila ta haramtawa jirage zuwa Gaza. A yanzu haka dai sojojin sun karkatar da jirgin ne zuwa tashar jirgin ruwa dake Ashdod.

Wani mai magana da yawun sojin Isra'ila ya ce ba'a samu wani tsaiko ba a lokacin da aka tare jirgin.

Jirgin ruwan mai suna Dignite na dauke ne da mutane 17, wanda suka hada da wani dan Majalisar Faransa da kuma wani dan jaridan dan kasar Isra'ila.