An tattauna tsakanin Amurka da Libya

Image caption Mu'ammar Gaddafi

Wadansu manyan jami'an gwamnatin Amurka sun gana da jami'an gwamnatin Libya.

An yi ganawar ce a kasar Tunisia.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce manufar ganawar ita ce a bayyanawa Shugaba Gaddafi cewa dole ne ya sauka daga kan mulkin kasar.

Shi kuwa kakaKin gwamnatin Libya, Ibrahim Moussa, ya ce tattaunawar matakin farko ne na gyara danganta tsakanin Amurka da Libya.

Manyan jami'an gwamnatin Amurkan da suka halarci wajen ganawar sun hada da tsohon jakadan Amurka a Libya Gene Cretz, da jami'in ma'aikatar harkonin wajen kasar, Jeffery Feltman.

Babu tabbaci game da jami'an da suka wakilci gwamnatin Libya a wajen tattaunawar.