Yaduwar cutar polio a arewacin Najeriya

Rigakafin cutar shan inna
Image caption Rigakafin cutar shan inna

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce an sake samun barkewar cutar shan inna ko kuma Polio a Najeriya, bayan da aka kusa kawar da ita daga kasar. Asusun yace, a bana yara 20 ne suka kamu da cutar a jahohi shida na arewacin kasar.

Hakan na nufin cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar a watanni bakwai na farko wannan shekara, ya kusa kai adadin da aka samu a bara - watau yara 21.

Asusun na UNICEF ya bayyana haka ne a yau, a wajen wani taron tattaunawa da shugabannin addinai da masu rike da sarautun gargajiya daga jahohi goma na arewacin Najeriyar.