Boko Haram: 'Yan sanda ba su amince da tuhuma ba

Image caption Ana zargin 'yan sanda da yiwa Muhammed Yusuf da Magoya bayansa kisan gilla

A Najeriya, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ci gaba da shari`ar da take yi wasu jami`an `yan sanda biyar ake zargi da yi wa shugaban Kungiyar Jama`atu Ahlissunna Lidda`awati wal Jihad da wasu mabiyansa kisan-gilla.

An karanta wadanda ake zargin tuhumce-tuhumcen da ake musu, amma ba su amince da aikatawa ba.

Laifuka biyu ne ake zargin jami`an `yan sandan da aikatawa, wadanda suka hada da kitsawa da aiwatar da ta`addanci, da kuma yi wa shugaban kungiyar jam`atu ahli sunnah Lidda`awati wal jihad, marigayi Mallam Muhammad Yusuf da wasu mabiyansu kisan-gilla a wani rikici da aka yi a shekara ta 2009 a garin Maiduguri.

An gurfanar da jami`an `yan sandan ne gaban alkali, wato da masu mukamin Mataimakin sufurtanda JB Abang da Akira, da Madu Buba da kuma wani mai mukamin babban sufurtanda, Mohammed Ahmadu da kuma Saja Adamu Gado, kana aka karanta musu jerin zarge-zargen da ake musu, amma kowannensu ya musanta.

Kazalika an gabatar da bukatar belin cikon mutum na biyar daga cikinsu wato Adamu Gado, kasancewar sauran an ba da belinsu tun a baya.

Saboda haka alkalin kotun mai shara`a Donatus Okorowo ya ba da umurnin a tsare shi a gidan wakafi zuwa lokacin da zai cika sharadin beli a ba shi, sharadin da ya hada naira miliyon goma da kuma mai tsaya masa da ya mallaki kadarar da ta kai miliyon goma a babban birnin tarayya.

A wannan gabar gurfanar da wadanda ake zargin gaba kuliya da kuma karanta musu jerin tuhumce-tuhumcen da ake musu dai za a iya cewa an fara shiga cikin harkar shara`ar gadan-gadan.

A wannan karon ma an girke jami`an tsaro a ciki da wajen harabar kotun, tare da yi wa masu shiga binciken kwakwa.