Majalisar dokokin Burtaniya ta yi suka ga 'yan sandan kasar

Image caption Wani dan sandan Burtaniya

'Yan majalisar dokokin Burtaniya da ke bincike game da zargin saurare da karanta sakon wayar mutane sun zargi 'yan sandan kasar da gazawa wajen gudanar da ayyukansu.

Kwamatin majalisar dokoki mai kula da harkokin cikin gidan Burtaniya ya ce rundunar 'yan sandan ta dauki ma'aikatan jaridar News of the World aiki bayan tana da masaniyar cewa suna leken asirin wayar jama'a

Kwamatin ya yi kira ga gwamnati ta kara himma kan binciken da take yi game da batun .

Kwamitin ya ce duk da yake rundunar 'yan sandan na gudanar da sabon bincike game da batun, sai dai hakan ba zai yi wani tasiri ba ganin cewa yawancin 'yan sandan na da kashin-kaji a jikinsu.