Cameron ya yi nadamar daukar Coulson aiki

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Fira Ministan Burtaniya, David Cameron a wata zazzafar muhawara a zauren Majalisa

Fira Ministan Burtaniya, David Cameron ya shaidawa 'yan Majalisar Dokokin Burtaniya cewa da yana da masaniya da bai dauki tsohon editan jaridar News of the World, Andy Coulson aiki ba.

Wanan ne karo na farko da Fira Ministan ya furta kalaman da suka yi kama da na neman afuwa, Ya ce: "Gaskiya na yi nadama, ina bada hakuri da irin hankalin da abun ya tada."

A cikin wata zazzafar muhawara da akayi a zauren Majalisar, Shugaban 'yan adawa na jam'iyyar Labour, Ed Miliband ya zargi Fira Ministan da nuna halin ko in kula a lokacin daya dauki Coulson aiki.

Mista Cameron ya katse ziyarar da yaki yi ne a wasu kasashen Afrika domin halartar muhawarar aka yi game da batun satar bayanai ta watar salula da Jaridar News of the World ta yi.

David Cameron ya ce kamata ya yi Mista Coulson ya fuskanci kowani irin hukunci da aka dauka akansa idan an same shi da hannu kan batu badakalar satar bayanai ta wayoyin salula a lokacin da yake aiki a Jaridar News of the World.

Cameron dai ya dauki Mista Coulson ne a matsayin mai gana da yawunsa kafin ya yi murabus saboda badakalar satar bayanan wayayoyin salula.