Gwamnatin Serbia ta cafke Goran Hadzic

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Goran Hadzic shine na karshe cikin wandanda ake tuhuma da aikata laifin yafi a Bosnia

Gwamnatin Serbia ta ce ta kama mutumin da ya rage cikin wadanda ake zargin da aikata laifin yaki a tsohuwar kasar Yugoslavia a shekarun 1990.

Goran Hadzic shine shugaban kabilar Sabiya a gabashin Croatia, kuma kotun hukunta manyan laifuka a Hague ta zarge shi da laifin cin zarafin bil'adama.

Hadzic ya boye ne na tsawon shekaru bakwai da su ka wuce, bayan an mikawa gwamnatin Serbia, sammacin cafke shi.

Shugaban Serbia, Boris Tadic ya ce kasarsa ta cimma duk wannan sharadi da aka gidaya mata.

A cikin wata sanarwa, Kungiyar Tarrayar Turai, tay yi marhabin da matakin da Serbia ta dauka, inda ta ce zai taimaka mata wajen shiga kungiyar.

An dai cafke tsohon shugaban sojin sebia, Ratko Mladic watanni uku da suka wuce.