Jamus da Faransa sun cimma matsaya akan Girka

Image caption Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy da na Jamus Angela Merkel

Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun cimma wata matsaya game da shirin sake ceto kasar Girka.

Za su gabatar da Kudurin ne kafin a fara taron gaggawar da za'a yi a nahiyar turai a ranar Alhamis, domin daukar mataki a saboda fargabar kada matsalar Girkan ta yadu.

Wakilin BBC Andrew Walker ya ce babu shakka kasar Girka na bukatar karin tallafi domin ta samu damar biyan basukan da ake binta.

Asalin shirin farko dai, na da nufin kasar ta koma kasuwar hada-hadar kudade domin sake karbar rance a badi, amma yanzu ta tabbata cewa hakan ba mai dorewa ba ne.

Za a kara harajin bankuna

A don haka ne kuma shugabannin kasashen Turai suka amince cewa akwai bukatar su kara daukar matakai.

Za a samu tallafi daga sabon rance daga kasashen da ke amfani da takardar kudi ta Euro da kuma ta hanyar sayar da wasu kadarorin gwamnatin kasar ta Girka.

Amma kuma suna bukatar gudummawa da kamfanonin bada lamuni masu zaman kansu.

Kuma abune mai matukar wahala a iya aiwatar da shirin ba tare da ya yi illa ga bankunan kasar ta Girka ba.

Kasashen Italiya da Spainiya ma....

Wata shawara da kuma ake tattaunawa a yanzu haka, ita ce ta fito da sabon haraji kan bankunan nahiyar Turai.

Wani abu da ya sauya fasalin rikicin a wannan watan, shi ne na matsin lambar da kasashen Italiya da Spain suka dora kan kasuwannin hada-hadar kudade.

Tattalin arzikinsu da kuma basukan da ake bin gwamnatocinsu ya zarta matuka na kasashen da ke karbar tallafi - wato Girka da Ireland da kuma Portugal.

Wasu masana na ganin halin da kasashen Italiya da Spain za su samu kansu a ciki nan gaba ka iya sauya rikicin ba ki dayansa.

Yana kuma karfafa tunanin da wasu ke da shi na rugujewar takardar kudin ta uro ba ki daya.