'Yan Kenya za su iya neman diyya daga Burtaniya

Image caption 'Yan Kenya hudu da su kayi zargin cewa an ci zarafin su.

Babbar Kotu a nan London ta yanke hukunci cewar wasu yan kasar Kenya su hudu zasu iya shigar da kara na neman gwamnatin Birttania ta biya su diyya.

Wannan dai ya biyo zargin gana musu azaba a lokacin da Burtaniyar ta murkushe wata tarzoma ta Mau-Mau a shekarun 1950 da 1960 a kasar Kenya.

Mai shari'a McCombe, ya bayyana cewar yan kasar Kenyar suna da hujja mai karfi, to amma hukuncin da ya yanke bawai yana nufin an ganawa mutane azaba ba ne.

Mutanen hudu, Maza uku da Mace daya, sun ce an gana musu bakar azaba, da cin zarafi harma da dandanke mazakutarsu.

Su dai mahukuntan da suka yi mulkin mallaka a kasar ta Kenya sun musanta wannan zargi.

Jinkiri

Lauyan 'yan kasar kenyan Martyn Day ya yi marhaban da hukuncin kotun inda ya ce wanan wani me tarihi

Ya ce; "Fiye da shekaru hamsin da suka wuce mutanen da nake karewa sun sha azaba a hanu gwamnatin turawa mulkin malaka ta Birtniya.

"An dan dake , kuma an ci zarafin su , kana an rika lakada musu duka, wadanan sune was saga cikin abubuwan da suka rika fuskanta yayinda da Birtaniyar ke kokarin ganin ta dakile fafukar da yan kasar ke yi na neman yancin Kenya.

"Mutanen da muke karewa sun shafe shekaru suna gwagwarmaya domin samun adalci akan abun da aka yi musu, sai dai Gwamnatin mu ta rika kokarin ganin cewa hakan be faru ba ." In ji Martyn Day

Wani gungun magoya bayan 'yan kasar Kenya na tsaye a wajen kotun Cikin su harda Dan Thea wanda dan uwansa da 'yar uwarsa sun yi gwagwarmaya tare da 'yan Mau Mau domin samar wa kasarsu 'yancin kai

Ya ce; "Ina farin ciki, sai dai abun kunya ne da wanan batu ya dauki tsawon lokaci.

"Hakan ba dai dai bane kuma ina fatan gwamnatin Burtaniya a yanzu ba zata bata lokaci ba wurin shawo kan wanan batu.

"Amma ina ganin kamar jira suke har sai lokacin da wadanan mutane zasu mutu, kuma hakan laifi ne." In ji Dan Thea

Matsaloli

Sai dai 'yan kasar Kenya da a yanzu sun kai shekaru saba'in ko tamanin nada kalubale da dama a gabansu wadanda ke shawo kansu kafin a iya shawo kan wanan batu gabaki daya.

Na farko dai sai an yi shari'a sanan za'a iya yanke hukunci akan ko za'a iya shigar da kara saboda wannan abu da ya faru kusan shekaru hamsin da suka wuce ne.

A bisa tsari, zarge zargen a wanan mataki kamata ya yi a ce an sauraresu a cikin shekaru uku.

Sai dai ko da sun yi nasara akwai matsalar cewa da dama daga cikin mutanen da suka yi aiki a Rundunar sojin Birtaniya da Gwamnati sun mutu.

Bugu da kari shi kansa alkalin ya nuna shakku akan yiwuwar ko karar zata maida hankali ne akan takardu saboda ba za'a iya yiwa muhiman mutanen da wanan abun ya shafa tambayoyi ba.