Shugaban Malawi ya ce ba zai sauka ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Malawi, Bingu wa Mutharika

Shugaban kasar Malawi, Bingu wa Mutharika, ya ki ya sauka daga mulki duk da cewa akalla mutane takwas sun rasa rayukansu a zanga zangar kin jinin gwamnati da aka kwashe kwanaki biyu ana yi.

A jawabin da yaiwa kasar, shugaba Mutharika ya ce ba wata matsala da za'a warware da tashin hankali, kuma zai yi magana da 'yan adawa.

Yac e a shirye yake yanzu fiye da ko yaushe na a tattauna.

Ya kuma yi kira ga 'yan adawa da shugabannin fararen hula dake kuka da gwamnati da su zo a zauna a tattauna.

Wakilin BBC da ke Lilongwe, babban birnin kasar ta Malawi, ya ce an kai hari kan gine ginan gwamnati. Rikicin dai ya fara ne kan haushin lakadawa wasu masu fafutukar kare hakkin bil adama da 'yan jarida duka.