Jirgi kiran Kumbon Amurka ya sauka lafiya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin ya sauka ne da asuba

Jirgin bincike na Amurka a sararin samaniya mai suna Atlantis ya sauka lafiya a cibiyar binciken sararin samaniya ta Kennedy dake Florida.

Kwamandan jirgin, Chris Ferguson ya ce zuwan jirgin ya sauya fahimtar dan adam game da duniya baki daya da kuma doran kasa. Jiragen binciken biyar sun yi tafiya ta kusan kilo mita biliyan guda, lokacin da suka kai taurarun dan adam sannan suka kaddamar da na'urar hangen nesa ta Hubble suka kuma taimaka wajen gina tashar sararin samaniya ta kasa da kasa.

Sai dai kuma wannan wani abin bakin ciki ne ga hukumar kula da sararin samaniya ta NASA, sabilida ma'aikatanta dubu hudu ne yanzu za su rasa aikinsu.