Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Rigakafin Yara

Image caption Ana digawa wani yaro ruwan, rigakafi

Wani sakamakon binciken da aka fitar a shekarar 2008, wanda hukumar kidaya ta Najeriya ta yi da tallafin hukumar raya kasashe masu tasowa ta Amurka USAID da hukumar kula da al'umma ta majlisar dinkin duniya UNFPA kan lafiyar' al'ummar kasar tare da yin la'akari da shekaru da jinsin su ya bayyana cewa kashi 23 cikin dari ne na yara 'yan shekara guda zuwa shekara daya da wata goma sha daya sun kammala rigakafin baki daya.

Alkaluman dai sun rubanya wanda aka samu a sakamakon irin wannan binciken da aka fitar a shekarar 2003 wanda ya nuna cewa an samu kashi 13 cikin dari na yaran da akayiwa rigakafin.

Sai dai binciken na baya-bayan nan wanda ya rarrabe kason yaran da suka samu yin nau'oin rigakafin ya kuma nuna cewa kashi 29 cikin dari na yaran kasar sam ba 'a yi musu rigakafin ba.

Yara kashi 38 ne cikin dari dake burane ne suka samu cikkaken rigakafi, idan aka kwatanta su da takwarorinsu na yankunan karkara da yawansu yakai kashi 16 ne cikin dari.

To a cikin yaran da suka samu cikaken rigakafin a cewar binciken na 2008, yankunan kudu maso yammaci da kudu maso gabshin Najeriyar ne ke dauke da kaso mafi tsoka na yawan yaran da suka sami cikkaken rigakafin.

Inda al'kaluma suka nuna cewa a sun samu kashi 43 cikin dari.

Sai dai arewa maso yammacin kasar ita ce koma-baya da kashi shida cikin dari na yaran da suka samu cikkakken rigakafi. Kuma jihohin Kastina da Jigawa nan ne ake da mafi karancin yaran da suka samu rigakafi, inda alkaluma suka nuna cewa yara kashi daya kacal ne cikin dari suka samu cikkaken rigakafin.

Yayinda jihar Osun ke da adadi mafi rinjaye na da kashi 59 cikin dari, sai jihar Ondo dake biye da kashi 58 cikin dari.

Ilimin iayaye mata dai na taka muhiimiyar rawa wajen amincewa su kai 'ya'ayansu ayi musu rigakafin cuttutuka.

Domin kuwa binciken dai ya kuma bayyana cewa kashi 61 cikin dari na yaran da suka samu cikakken rigakafin iyayensu mata sun samu karatun gaba da firamare, yayin da kashi bakwai cikin dari kuma iyayensu ba su da ilimin boko sam-sam.

Shirin mu kenan na wannan makon. Ayi sauraro lafiya.