Rundunar tsaron Najeriya sun musanta cin zarafin jama'a a Maiduguri

Rundunar tsaro ta hadin gyiwa ta JTF, a Maiduguri na jihar Bornon Najeriya ta tabbatar da cewar tana ci gaba da yin tambayoyi ga wasu mutanen da ta kama wadanda ta ke zargi da tada bama bamai da kuma kisan jama'a.

Rundunar ta kara da cewar da zarar ta kammala bincike ta kan saki wadanda ta gano cewa ba su da laifi.

Kungiyar Jama'atu Ahlus Sunna Lid-da'awati wal Jihad, wadda ake kira Boko Haram, ta yi barazanar kai hari muddin dai ba'a saki 'yan kungiyarta da aka kama ba.

Laftana Kanar Hassan Ifijeh Mohammed , kakaakin rundunar, ya kuma musanta zargin cewar rundunar na wuce makadi da rawa wajen gudanar da aikinta a birnin.