Haramcin karbar agaji daga wasu kungiyoyi na nan daram- Inji Al-Shabaab

Kungiyar al-Shabab ta mayar da martani
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana fama da karancin abinci a Somalia

Kungiyar 'yan gwagwarmayar Isalaman nan a Somalia, wato al-Shabaab, ta ce ba ta dage haramcin da ta yi wa wasu hukumomin bada agaji na kasashen waje a manyan wuraren dake karkashin ikonta a kasar ba.

Wani mai maga na da yawun kungiyar ta al-Shabaab ya ce Majalisar Dinkin Duniya na zuzuta maganar fari ne a kudancin Somalia.

Duk da cewa har yanzu wasu kungiyoyin kasashen waje na ayyukansu Somalia ta hanyar kungiyoyin bada agaji na kasar, hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya na daga cikin manyan kungiyoyin da aka haramtawa aiki a wajen.

Sheikh Ali Raage ya zargi kungiyoyin bada agajin da Majalisar Dinkin Duniya da shigar da siyasa cikin matsalar karancin abincin da ake fama da shi a Somalia, domin sanyaya gwiwar jama'a da neman shigar da su addinin Kirista.

'Dole ne mu dauki mataki'

"Kungiyoyin agajin da muka dakatar a baya ba sa cikin wannan sassaucin, ba wai yanzu ba harma nan gaba.

"Muna magana ne a kan wadanda dama suke aiki a kasar. Wasu daga cikin wadanda muka dakatar sun shiga cikin al'amuran siyasa ne. Wasu kuma na rusa rayuwar jama'armu ne. Don haka dole ne mu dauki mataki".

Sheikh Ali Raage ya kuma yi watsi da batun cewa ana fama da matsananciyar yunwa a Somalia, yana mai cewa Majalisar Dinkin Duniya na zuzuta lamarin ne, kuma ikirarin da take yi na neman agaji farfaganda ce mara tushe.

Ya ce babbar matsalar na kan Majalisar Dinkin Duniya.

"Rahoton da suka bayar na baya ya nuna cewa akwai matsalar yunwa a Somalia. Amma muka ce ba haka bane. Babu alamun gaskiya a ciki ko kadan.

"Ana fama da fari da karancin ruwan sama a Somalia, amma bai kai munin yadda suke zuzutawa ba".