Wani bam ya tashi a Maiduguri

Wani bam ya fashe a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno na Najeriya.

Bam din dai ya tashi ne a wata kasuwa dake tsakiyar birnin, inda rahotanni ke nuna cewa wuta na ci gaba da ci a kasuwar sakamakon fashewar bam din.

Ko a jiya ma sai da aka samu fashewar wasu bama baman har sau biyu a wasu unguwannin dake birnin.

Tuni dai jami'an tsaro na hadin gwiwa ta JTF suka danganta fashewar wannan bam din kan kungiyar na ta Jama'atu Ahlil Sunna lid'daawati, da aka fi sani da suna Boko Haram, wadda take kai hare hare a birnin.