An yi wa mata 50 fyade a kasar Congo

Congo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu mata da aka yi wa fyade a wani asibiti a Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dakarun sojin kasar Congo sun yi akalla mata hamsin fyade a wani kauye da ke Gabashin kasar a farkon shekaran nan.

Wannan shi ne karo na biyu da aka binciki batun fyade a yankin a lokaci guda.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kalla mata 47 ne dakarun gwamnati suka yi wa fyade a kauyen Bushani da ke Arewacin Kivu daga ranar 31 ga watan Disamba zuwa 1 ga watan Janairu.

Ta ce sojojin Congon sun kai hari a kauyen da adduna da bindigogi da rokoki da kuma gurneti suna masu fakewa da farautar 'yan tawaye - sun sace ko kuma lalata gidaje akalla dari.

Adadin ka iya fin haka

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin matan da aka yi wa fyaden ka iya fin haka, saboda wasu da ke tsoron abinda ka iya biyo baya sun ki ganawa da masu binciken.

Sai dai Majalisar ta ce bata da tabbaci ko sojojin da suka aikata abin na cikin wadanda suka samu tallafi daga shirin samar da zaman lafiya a kasar.

Rahoton ya nuna yadda ake samun karancin hadin kai tsakanin dakarun gwamnati da masu bincike na soji.

Ministan yada labarai na kasar Lambert Mende ya shaida wa BBC cewa mahukunta za su duba zarge-zargen.

A kwanakin baya aka samu wasu sojoji 9 da laifin yiwa mata 50 fyade a bikin ranar sabuwar shekara a kusa da Gundumar Kudancin Kivu, yayin da ake ci gaba da bincike kan wani zargin fyaden da ya shafi wasu mata 170.