Mutane fiye da 90 ne suka mutu a harin kasar Norway

Mutane 87 sun mutu a kasar Norway Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rabon Norway da fuskar bala'i irin wannan tun yakin duniya na biyu

'

'Yan sanda a Norway sun tuhumi wani mutum mai shekaru talatin da biyu dan kasar ta Norway da laifin kai hare hare biyu da suka yi sanadiyar mutuwar mutane akalla casa'in da daya, karkashin dokokin yaki da ta'addanci.

Sunan wanda ake zargin, dai shi ne, Anders Behring Breivik.

Pirayim Ministan kasar ya ce,"Norway 'yar karamar kasa ce, amma kanmu hade yake, muna kuma taya dukkan wadanda wannan abu ya shafa alhini, kan abin da ya faru a Oslo da kuma sansanin matasa."

Mutane tamanin da hudu ne suka mutu, galibinsu matasa lokacin da wani dan bindiga cikin kayan 'yan sanda ya bude wuta a wajen taron matasa da jam'iyyar Labour ta shirya, kusa da Oslo.

Sa'o'i biyu kafin nan, wani harin bam a ofishin gwamnati a Oslo ya halaka mutane bakwai.

Ya tsallake rijiya da baya

Wani dan bindiga sanye da kayan 'yan sanda ya bude wuta a wani sansanin matasa da ke tsibirin Utoeya a kusa da garin Oslo - daruruwan mambobin jam'iyyar Labour da ke mulkin kasar ne suka taru a wajen.

Yara da dama sun rika fadawa cikin ruwa a kokarin neman mafaka, inda a yanzu mahukunta suka ce akalla mutane 80 ne suka mutu.

Sa'o'i kadan kafin harbe-harben, wani shirgegen bom ya tashi a tsakiyar birnin Oslo, an ji karar fashewar a ko'ina cikin birnin inda ta girgiza gina-ginen gwamnati, ciki harda ofishin Fira minista.

Fira Minista Jens Stoltenberg, wanda aka nufa da harin ya tsallake rijiya da baya.

Wadanda suka ga abin da ya faru sun dimauta matuka, 'yan sanda sun shawarci Fira Ministan da kada ya bayyana inda yake lokacin da ya bayyana a gidan talabijin domin yiwa jama'ar kasar bayani.

'Muna da rawar takawa'

Shugaba Obama na Amurka ya ce harin wata matashiya ce da ke nuna cewa duniya na da rawar takawa wajen hana hare-haren ta'addanci:

"Bamu da cikakken bayani kawo yanzu, amma ina mika jimami na ga jama'ar kasar Norway, kuma wannan na tunasar da mu cewa kasashen duniya na da rawar takawa wajen hana irin wadannan hare-haren na ta'addanci afkuwa.

Ana saran Fira Ministan kasar zai halarci tsibirin na Utoeya a yau, kawo yanzu babu tabbas kan wanda ya shirya wannan harin, sai dai an kama wani mutum da ake kyautata zaton maharin ne - dan dai kasar ta Norway ne.

Kuma 'yan sanda na alakanta shi da harin bom.