Tallafi ga 'yan gudun hijirar Libya

Yan gudun hijirar Bangladeshii
Image caption Akwai kimanin 'yan Bangladesh 25,000 da ke aiki a Libya yanzu haka

Gwamantin kasar Bangladesh za ta fara kaddamar da wani shiri na bada tallafin kudi ga dubban ma'aikata 'yan kasar da suka yo kaura daga kasar Libya a farkon bana.

Kimanin ma'aikata dubu 36 ne 'yan kasar ta Bangladesh aka tilastawa barin Libya tare da sauran ma'aikatan kasashen waje sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi a kasar.

Dubban 'yan Bangladesh din sun shafe makonni a kan iyakar kasar Masar da Tunisia kafin daga bisani a kwashesu zuwa gida.

Wakilin BBC Anbarasan Ethirajan a birnin Dhaka, ya ce har zuwa lokacin da fada ya barke a kasar Libya, kasar ta kasance wani dausayi ga dubban 'yan cirani daga kasar Bangladesh.

Tallafin dala 700

Akwai fiye da 'yan Bangladesh 60,000 a Libya, inda mafi yawansu ke aiki a kamfanonin gine-gine da kuma na man fetur. Kuma danginsu da ke gida sun dogara ne kan kudaden da suke aika musu.

Sai dai jim kadan bayan barkewar rikici a kasar, sai aka fara kaiwa ma'aikatan kasashen waje ciki harda 'yan kasar Bangladesh hari - kuma da dama daga cikinsu sun fice daga kasar.

Yawancin 'yan Bangladesh din sun koma gida ne ba tare da ko sisiba inda suka bukaci gwamnati ta tallafa musu domin sake gina rayuwarsu.

A yanzu gwamnati ta ji kukansu, kuma ta kirkiro wani shiri na baiwa kowannensu tallafin kudi na dala 700 bayan an tantance shi.

'Ina murna da wannan tallafi amma....

Sai dai mutane irinsu Delawar Hossain, wanda ya dawo daga Libya a watan Maris, ya ce kudin ba za su isa ya mayar da abin da ya rasa ba.

"A yanzu da tattalin arzikin kasarmu ya tabarbare, kuma bani da aikin yi. Ina murna da wannan tallafi amma na kashe kudade da dama wajen neman aiki a Libya, don haka ina bukatar kudi domin biyan bashi".

A yanzu haka ana saran akwai 'yan Bangladesh 25,000 da ke aiki a Libya.

Fita kasashen waje domin aiki dai, na daga cikin hanyoyin samun kudaden shiga na kasashen waje ga kasar ta Bengladesh.