Mutane kusan arba'in ne ake cewar sun bata a wani hari a Maiduguri

Rahotanni daga garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno ta Najeriya na cewa farar-hula da dama ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu mutanen kuma suka bace.

Kazalika motoci da shaguna da ba a bayyana adadinsu ba sun kone kurmus, jim kadan bayan wani tashin bom da ya abku a unguwar Budum da marecen jiya, wanda ya jikkata jami'an soji uku.

Wasu mazauna unguwar na zargin cewa lamarin ya auku ne sakamakon harbin kan mai uwa da wabin da rundunar da ke tabbatar da zaman lafiya a jihar ta rika yi bayan da sojojinta suka fusata, amma rundunar ta musanta.