Kungiyar Izala ta nemi a yiwa Najeriya addu'a

Tswirar Najeriya
Image caption Tswirar Najeriya

Kungiyar Musulunci ta Jama'atu Izalatil Bid'ah wa Ikamatis Sunnah a Najeriya ta nuna damuwa a game da matsalolin tsaron da ke addabar kasar.

Kungiyar ta bukaci dukkan malamai a kasar su dukufa wajen yin addu'o'i domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali .

Kiran ya biyo bayan babban taron da kungiyar ta gudanar ne a Kaduna, domin nazarin irin gudunmawar da za ta bayar wajen samar da zaman lafiya, yayinda ake shirin fara azumin watan Ramadan.