Shin ko wanene ya kai haria a Norway?

Anders Behring Breivik Hakkin mallakar hoto
Image caption Behring Breivik ya ce yana da ra'ayin rikau na kin jinin Musulunci

An samu karin haske kan ko wanene Anders Behring Breivik, mutumin da ake zargi da kai hari a kasar Norway. Ya bayyana cewa yana da ra'ayin rikau na kin jinin musulunci.

Wadanda suka bi diddigin rubuce-rubucensa a shafin intanet ma, sun ce yana da tsattsauran ra'ayin siyasa. Mutumin wanda kafafan yada labarai suka bayyana da suna Anders Behring Breivik, ba shakka dan kasar Norway ne, baya ga yadda yake zaune a cikin jama'a, 'yan sanda sun ce kalaman da ya wallafa a intanet na baya-bayan nan sun nuna cewa yana da ra'ayin rikau na kin jinin musulunci.

Hans Ferguson wani dan jarida da ke aiki da jaridar Pigi:

"Na gayawa mutane cewa mutumin da ake zargin yana da rikakkiyar adawa da gwamnatin jam'iyyar Labour, kan abin da ya ke gani kamar sakaci ne wajen fuskantar kungiyoyin musulmai.

Amma ina ganin babu wanda zai goyi bayansa akan wannan aika-aikar.

Kirista ne mai tsattsauran ra'ayi

Ya bayyana a shafinsa na Facebook wanda yanzu aka cire daga intanet, cewa shi kirista ne mai tsattsauran ra'ayi.

Ya taso ne a birnin Oslo, sannan ya fita domin kafa gonar lambu.

Wani da ake wa kallon karamin manomi, yanzu ya ce ya sayi ton shida na sinadarin taki - wanda ake amfani da shi wajen hada bom.

A yanzu 'yan sandan Norway sun ce mutumin da suke zargin ya amsa wasu daga cikin abubuwan da ake zarginsa da aikatawa.

Babban abin tambayar shi ne dalilin da ya sanya shi yin abinda ya yin? Da kuma ko yana aiki ne tare da wasu gungun jama'a da ke shirin kaddamar da makamantan wannan hari a gaba.