Kungiyar Red Cross ta kai agaji a Somalia

Daya daga cikin yaran da ke fama da tamowa a Somalia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Daya daga cikin yaran da ke fama da tamowa a Somalia

Kungiyar agaji ta Red Cross ta samu sukunin kai abinci a daya daga cikin yankunan kasar Somalia da matsalar fari ta fi shafa.

Kungiyar Red Cross, wadda ke aiki da wani kwamiti a yankin, ta samar da abinci ga mutane dubu ashirin da hudu, a wani yanki dake karkashin ikon kungiyar kishin Islama ta al-Shabaab.

An raba kayayyakin ne , wadanda suka hada da wake da shinkafa da kuma man girki, ga iyalai a garin Baardhere, a arewa maso yammacin Mogadishu, babban birnin kasar.

Wannan kai kayan agaji na nuna cewar, duk da al-Shabaab ta hana wasu kungiyoyi kai agajin abinci, a yankunan dake karkashinta, akwai sauran kungiyoyin da ke iya gudanar da ayyukansu a can.