'Ya kamata Amurka ta warware matsalar basusukan ta'

Shugaba Barack Obama Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Barack Obama

Asusun bada lamuni na IMF ya yi wa Amurka kashedin ta gaggauta yin wani abu game da bashin da yayi mata kanta.

Asusun ya ce, idan ba haka ba kwa, to tattalin arzikinta zai shiga garari.

A cewar IMF, idan 'yan majalisar dokokin Amurkar basu amince da bukatar shugaba Obama ta karin haraji ba, to cibiyoyin kudin duniya zasu ji a jikinsu.

Sai dai sakatariyar harkokin wajen Amurkan, Hilary Clinton, tace tana da kwarin gwiwar cewa majalisar dokokin kasar zata cimma daidaito akan maganar, kuma ta kawar da duk wani haufi akan durkushewar tattalin arzikin Amurkan.