'Ina son a daure Dominique Strauss-Khan': Nafissatou

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dominique Strauss-Khan

Ma'aikaciyar hotel din nan da ta zargi tsohon shugaban asusun ba da lamuni na duniya da yunkurin yi mata fyade a New York ta ce za ta so ta ga ya yi zaman kaso.

A jawabinta na farko a bainar jama'a a kan batun, Nafissatou Diallo ta ce abin da ta fada ya wakana tsakaninta da Dominique Strauss-Kahn a watan Mayu gaskiya ne.

Jawabin nata ya zo ne a daidai lokacin da hukumomi ke tunanin janye tuhume-tuhumen da ake yiwa Mista strauss-Kahn saboda shakkun da ake nunawa a kan ingancin maganganunta.

A wata sanarwa da suka fitar, lauyoyin Mista Strauss-Kahn sun bayyana jawabin matar da cewa abin dariya ne kuma abin da ya wakana tsakanin ta da wanda suke karewa ya faru ne bisa amincewar junansu.