An kara kudin shiga jiragen sama a Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Yanzu haka a Najeriya kudin shiga jiragen sama ya karu da wajen kashi hamsin cikin dari a kowacce tafiya daya a cikin kasar.

Kamfanonin jiragen sama sun bayyana cewa karin kudin jirgin ya zama dole a sakamakon tashin gwauron zabin man jiragen sama da kuma kudaden haraji da suke biya ga hukumomin jiragen sama a kasar.

Hakan ya sa wasu fasinjoji na fadin cewa zasu maida hankali wajen tafiya da mota sabida karin ya yi musu yawa.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti don duba wannan matsala.