Takaddama kan zargin kama sojoji a Nijar

Wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a a Nijar sun nemi gwamnati da ta fito ta yi bayani game da zargin kama wasu hafsoshin soja biyar.

Kungiyoyin, ciki har da MONSADEM, sun ce bisa la'akari da zargin da ya gama gari na yunkurin halaka shugaba Muhammadou Issofou, da kuma juyin mulki, lallai akwai bukatar a sanar da 'yan kasa halin da ake ciki.

Kungiyoyin sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka kira.

Su dai hukumomin ba su tabbatar da labarin ba, ba su kuma karyata shi ba.