Bankin Duniya zai bada dala miliyan 500 domin magance fari

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Akalla wajen mutane miliyan 11 ke fama da fari, sanadiyar yunwa

A yayinda ake taron gaggawa kan fari a birnin Rome na kasar Italiya, Bankin Duniya ya ce zai samarda da sama da dala miliyan dari biyar domin magance fari a kasashen dake gabashin kusurwar Afrika.

Za'a yi amfani da kudaden ne wajen magance fari daga kasar Djibouti zuwa Kenya.

Hukumar samarda abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce ta shirya wani taro ne akan fari a Rome domin bullo da hanyoyin taimakawa wajen sama da mutane miliyan goma sha daya dake bukatar taimakon gaggawa sanadiyar fari.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yankuna biyu a kudancin Somalia a matsayin wuraren dake fama da matsananciyar yunwa.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon, ya yi kira ga kasashen duniya dake bada agaji, domin samarda karin wajen dala biliyan daya da miliyan dari shida wajen agaji.