Mutane 76 sun mutu a Morocco sanadiyar hadarin jirgin sama

Image caption Tawirar kasar Morocco

Rahotanni daga Morocco na cewa akalla mutane 76 ne suka mutu bayan wani jirgin soji ya rikito akan wani tsauni a kudancin kasar.

Kamfanin dilancin labaran Morocco ya ce mutane da dama ne suka mutu a hadarin a lokacin da jirgin ya ke kokarin sauka a kusa da yankin nan na yammacin sahara da ake takaddama akansa.

Jirgin kirar Herculus c130 na dauke ne da kimanin mutanen 70, yawancin su sojoji ne da iyalansu.

Jami'an sojin kasar dai sun alakanta hadari ga rashin kyawun yanayi.

Jirgin na dauke da mutane 81 ne cikin har da ma'aikatan jirgin tara da sojoji 60 da kuma fararen hula 12.

An dai gano gawawwaki 42, kuma har yanzu ana neman sauran.