'Breivik na da tabin hankali' - Lauya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lauyan da ke kare Mista Breivik, Geir Lippestad

Lauyan da ke kare mutumin da ake tuhuma da kai hare-hare a Norway, wato Anders Behring Breivik, ya ce mai yiwuwa wanda yake karewan na da tabin hankali.

Har wa yau lauyan ya ce bai sani ba ko Breivik zai amince yana da tabin hankali a gaban kuliya.

Lauyan ya ce bincike ya nuna cewa Breivik ya sha wadansu haramtattun kwayoyi kafin ya kaddamar da hare-haren.

Hare-haren dai sun yi sanadiyar mutuwar mutane 76, kuma Mista Breivik na fuskantar tuhumar aikata laifin ta'addanci.

Lauyan Mista Breivik, Geir Lippestad, ya shaidawa 'yan jarida cewa: "Ina ganin wannan al'amarin dai na nuni da cewa yana da tabin hankali."

'Yan sanda

Ministan Shari'a na kasar Norway ya yabi matakan da 'yan sandan kasar suka dauka a lokacin da aka kai hare-hare a kasar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 76, a ranar Juma'ar da ta gabata.

Ministan, Knut Storberget, ya ce 'yan sanda sun yi matukar kokari, duk da cewa dai, kafafen yada labarai na sukansu da cewa basu dau matakan gaggawa ba lokacin da ake kai harin a tsibirin Utoeya.

Har yazu dai 'yan sandan na bincike a tsibirin Utoeya da kuma inda aka kai harin bam din a cikin birnin Oslo.

'Yan sandan kasar dai na tunanin tuhumar maharin da aikata babban laifi kan bil-Adama domin a daure shi na tsawon lokaci a gidan kaso.

Makoki

Fiye da mutane dubu dari ne suka taru a tsakiyar Oslo, babban birnin kasar ta Norway, don tunawa da wadanda suka mutu a hare-haren.

Yawancin mutanen da suka taru din dai na rike da furanni, suna rungumar juna cikin wani yanayi mai sosa rai.

Yanzu dai 'yan sanda na gudanar da bincike don gano ko da hannun wasu a cikin harin, bayan wanda ya kai harin ya ce ba shi kadai ya kitsa shirya shi ba.

Mista Breivik ya ce tabbas shi ne ya kai harin, amma ya ki amsa laifin aikata ta'addanci.