Gwamnatin Burtaniya ta amince da 'yan tawayen Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sakatare harkokin kasashen wajen Burtaniya, William Hague

Sakataren kasashen wajen Burtaniya, William Hague, ya ce gwamnatin Burtaniya za ta amince da shugabancin gwamnatin rikon kwarya ta 'yan tawaye a Libya a matsayin halastacciyar gwamnati.

Wannan dai ya biyo bayan amincewar da kasar Amurka da kuma Faransa suka yiwa gwamnatin 'yan tawayen kasar ta Libya.

Mista Hague ya ce Burtaniya za ta mika goron gayyata ga 'yan tawayen domin su nada jakadan su a birnin Landan.

An dai sallami duk wakilan da gwamnati Kanal Gaddafi ta nada a wadannan kasashe.

Har wa yau Burtaniya ta mikawa 'yan tawayen wajen dala miliyan dari da hamsin na man kasar da ta kwace daga gwamnatin Kanal Gaddafi.

Burtaniya dai tana kan gaba-gaba cikin kasashen NATO da ke kaiwa gwamnatin Kanal Gaddafi hari.