Karin wa'adin mulkin Najeriya ya fara janyo cece-kuce

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A Najeriya, Shugaba Goodluck Jonathan ya fitar da wata sanarwa wadda a cikinta ya ce zai mika bukatar yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin sauya wa'adin mulkin shugaban kasa da kuma gwamnoni zuwa wa'adi guda amma na fiye da shekaru hudu.

Tun a cikin makwannin da suka gabata ne dai wasu kafofin yada labarai ke cewa, shugaban kasar zai nemi a maida wa'adin mulkin ya koma wa'adi daya tal.

Sai dai kuma Shugaba Jonathan ya ce, ba ya cikin wadanda za su amfana da wannan sabon tsari idan an yi shi.

Tuni 'yan adawa da masu sharhi kan siyasar kasar suka fara tofa albarkacin bakinsu game da wannan batu.

Yan adawar dai sun ce wannan wani mataki ne da shugaba Jonathan ke son yayi amfani da shi domin ya tsaiwata wa'adin mulkinsa.

Su kuwa masu sharhi kan harkar siyasa sun ce hakan be basu mamaki ba saboda kusan tun bayan zaben Aprilu, daga take- taken shugaban kasar da kuma mukarabansa aka fara ganin alamun zasu kara wa'adin mulkinsu.