Shekara guda cif kafin a fara gasar Olympic a Landan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filin wasan Olympic

A kowanne shekaru hudu ne ake gasar Olympics, kuma bayan wanda akayi a Beijing na kasar China a shekara ta 2008, sauran shekara guda cif a fara wata sabuwar gasar ta Olympics da birnin London zai dauki bakunci a badi.

Wadanda ke shirya bukin sunce komai na tafiya dai dai kamar yadda aka tsara.

Paul Deighton Shugaban kwamitin shirya gasar yace haryanzu da sauran aiki, amma kuma yana alfahari da yadda abubuwa ke tafiya.

Shugaban kwamitin ya shaidawa BBC cewa baza'a samu matsala ba wajen samarwa jama'a tikitin shiga kallon wassanin.

Komi na tafiya daidai

Ya ce; "akwai tikiti masu yawa kuma mutane na son suyi ta tanadinsu, sai mukayi tunanin cewa ayi kuri'a, don haka ne hanya mafi a'a la da zamu samarwa mutane tikiti."

Sai dai wasu na ganin cewa abun na 'yan boko ne kawai kuma akwai almubazzaranci a ciki.

An kashe dala biliyan 15, akan shirye-shiryen, abunda ya zarta kasafin da akayi tun farko.

A lokacin gasar dai, 'yan wasa 10,500 ne zasu fafata daga kasashe 200.

Zasu kuma samu rakiyar jami'ai da masu horaddasu kusan kimanin 5000.

Ana sa ran halartar manema labarai har su 20,000 da dubbban 'yan kallo daga kasashe daban daban na duniya.

Za a kuma shafe kwanaki 17 ne ana fafatawa a wasanni 26 a yayinda za a bada kyautuka guda 300.

A matakin soma bikin, an soma kidayan kwanakin da suka rage a dandalin Trafalgar wato 'count down'.