Kungiyar Taliban ta kai hari a Afghanistan

Ma'kacin BBC da aka kashe Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hare-hare suna kara kamari kwanan nan

'Yan kungiyar Taliban sun kai wani gagarumin hari a yammacin Afghanistan, inda suka yi amfani da 'yan kunar bakin wake biyu, da makaman roka da bindigogi masu sarrafa kansu.

Sama da mutane ashirin ne aka kashe a hare-haren, ciki har da wani wakilin BBC Ahmad Omid Khpolwak.

An kai hare-haren ne kan ofisoshin mataimakin gwamnan lardin Uruzgan da ke barnin Tarin Kot, da hedikwatar 'yan sandan lardin, da kuma wani kamfanin masu aikin gadi na wani babban kwamandan lardin mai karfin fada aji.

‘Yan taliban din sun kwashe kimanin sa'o'i biyar suna ba ta-kashi da jami'an tsaron Afghanistan, wadanda dakarun NATO suka taimaka mawa ta sama.