Hadarin jirgin kasa na kasar China

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wurin da harin jirgin kasan ya auku

Firaministan China Wen Jiabao, ya yi alkawarin cewa binciken da za'a gudanar a kan hadarin jirgin kasan da ya auku a makon da ya gabata zai kafa tarihi.

Yayin da ya ke jawabi a wurin da hadarin ya auku, inda akalla mutane talatin da tara suka rasa rayukansu, wasu kusan dari biyu kuma suka jikkata, Mista Wen ya ce kare rayukan al'umma ne babban burin gwamnati.

Tun da farko dai jami'an hukumar jiragen kasa ta China sun ce wata waya a na'urorin ba da hannu ce ta haddasa hadarin a kusa da garin Wenzhou da ke gabashin kasar.

A cewarsu, wata na'urar ba da hannu ce ta gaza sauyawa zuwa launin ja bayan tsawa ta fada mata, al'amarin da ya sa wani jirgin kasa mai saurin gaske ya yi taho mu gama da wani jirgin wanda ya kakare.