An kashe kwamandan 'yan tawayen Libya

Hakkin mallakar hoto wikipidia
Image caption Abdel Fattah Younes

Shugaban 'yan tawayen Libya Mustafa Abdul-Jalil ya bayar da sanarwar kashe kwamandan sojojinsu Janar Abdel Fattah Yunus.

Mista Abdul-Jalil, ya ce wasu 'yan bindiga ne suka kashe Janar Yunus bayan da aka bukaci ya dawo daga fagen daga don ya bayyana a gaban kwamitin Shari'a.

Shi dai Janar Yunus shi ne ministan harkokin cikin gida na Kanal Gaddafi kafin a fara bore a wata Fabrairu lokacin da ya bijire wa gwamnati inda ya koma bangaren 'yan tawayen.

'Yan tawayen dai basu amince da shi sosai ba, kana gwamnatin Gaddafi na yi masa kallo a matsayin wanda ya ci amanar kasa.