Ana fafatawa a Somalia a yayin da ake kai agaji

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kusan mutane miliyan goma sha daya ne ke fama da matsananciyar yunwa

An fara fafatawa a babban birnin Somalia, Mogadishu, kwana guda bayan da shirin Samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya fara kai agajin abinci ga dubbin mutanen kasar dake fama da matsananciyar yunwa.

Mutane da dama ne suka mutu, a lokacin da sojojin gwamnati wanda dakarun sojin tarrayar Afrika ke marawa baya su ka kai a hari kan wuraren da kungiyar Islama ta Al-Shabab ke da iko.

Kungiyar Tarrayar Afrika ta ce, mayakan al-shabab 41 ne suka bada kai a lokacin harin a yayinda kuma gwamnati ta kwace wannan yankin da suke.

Wakilin BBC a gabashin Afrika ya ce harin da dakarun gwamnati ke kaiwa wani yinkuri ne na bari a shigo da adaji a wasu wurare a birnin na Mogadishu.

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fara kai kayan abinci ta jirgin sama zuwa Mogadishu, babban birnin Somalia a ranar Talata.

Hukumar ta kai tan goma na abinci mai kara kuzari daga Kenya don ciyar da yara kanana masu fama da bala'in yunwa.

Hukumar ta kuma ce za ta ciyar da yara dubu uku da dari biyar har na tsawon wata guda.

Kuma wannan shi ne sawun farko a sawu goman da aka shirya yi na kai kayan abincin ta sama.