Wasu kasashen Larabawa sun gaza ba Somalia agaji

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kusan mutane miliyan goma sha daya ne ke fama da matsananciyar yunwa, yawancinsu yara.

Shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya ya fadawa BBC cewa, Saudi Arabia ta ce za ta ba da tallafin dala miliyan hamsin domin samar da abinci ga 'yan gudun hijirar Somalia.

Wannan sanarwa dai ta zo ne bayan Sakatare Janar na Majalisar ta dinkin duniya, Ban Ki Moon, ya yi kira ga Saudiyya da kuma kasashen yankin Gulf su kara tallafin da suke bayarwa ga kasashen gabashin Afirka wadanda ke fama da bala'in fari.

Kafin yanzu dai, kasar hadadiyar daular larabawa na daya daga cikin manyan kasashen labarawa da tabi baiwa hukumar samar da abinci na majalisar Dinkin duniya agaji kudin domin taimakon kasar Somalia.

Wannan kudi wanda ya kai wajen kasa da dalan Amurka miliyan biyu, ya sa kasar baya a sahun kasashen kamar su Ireland da Switzerland wajen bada agaji.

Nuna banbanci

Kuwait dai ta yi alkawarin bada miliyan goma, amma sauran kasashen Labarawa basa wani yunkurin bada wani taimakon agaji ba.

Ana ta dai sukar matakin da kasashen larabawan su ka dauka na nuna halin ko' in kula ga matsalolin da ake fuskanta a wata kasar Musulmi, kuma member a kungiyar kasashen larabawan.

Akwai banbancin da ake yawan nunawa ga kasar Somalia, daga kasashen larabawa ganin mutanen kasar bakar fata ne, kuma basu da alaka da kasashe kamar su Saudiyya da kuma Kuwait.

Abun da wannan ke nuni anan shine yawancin kasashen dake gabashin Afrika, sun zama bayi ga wadannan kasashen labarawa a baya, kuma za'a iya cewa har yanzu suna kyamar su.

Watan Ramadan

Ganin cewa ana gab da azumi kuma lokacin taimako ne ga kasashen larabawa, ganin irin hotunan dake fitowa daga kasar Somalia a akwatunan talbiji akwai yiwuwar shugabanin kasashen larabwa su taimaka wajen bada agajin ga mutanen dake fama da yunwa saboda irin matsin lambar da za su fuskanta.

Agajin dala miliyan hamsin da kasar Saudiya ta bada ya sanya ta a bayan Amurka a cikin jerin kasashen da sukafi bada agaji.

Wani jami'in hukumar samarda abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce yana da kwarin gwiwar cewa kasar Saudiya za ta sauke nauyi alkawarin da ta dauka.

A shekarar 2008, kasar Saudiyya ce ta bada kusa wajen rabin dala biliyan guda wa hukumar wanda ya zuwa yanzu babu kasar da aka samu da ta bada irin wanan gudunmuwa.